Majalisar Masarautar Shuwa Arab, Lagos

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar masarautar Shuwa Arab, Lagos



Gabatarwa

Majalisar Sarkin Shuwa Arab na Jahar Lagos ta ƙunshi muƙaman sarautu da suka haɗa da:

  1. Sultan: Shi ne shugaban wannan Masarauta. Kujerarsa ita ce sama da kowace kujera a duk faɗin wannan masarauta. Hukuncinsa shi ne na ƙarshe a wannan fada. Yana yanke hukunci ko ɗaukar mataki a kan wani lamari ko wata magana bisa shawarar da majalisa ta zartar tare da neman shawara ta musamman ga mashawartansa na musamman idan buƙatar hakan ta taso.
  2. Waziri: Mutum na biyu a daraja a wannan masarauta shi ne waziri, wanda yake a matsayin mataimakin sarki. Wanda yake hawa kujerar sarki idan sarki baya gari ko kuma bisa wakilcin sarki.

    Wannan muƙami na waziri an raba shi gida biyu; waziri da kuma wakili. Shi kuma wakili shi ne yake kula da sauran al’amuran da suka shafi al’ummar Shuwa da ke cikin birnin Lagos.

  3. Galadima: Shi ne jami’i mai kula da harkokin manyan baƙi a duk lokacin da ya zama ana da wani muhimmin taro ko biki a wannan masarauta. Samar da masauki, abincin baƙi da sauran al’amuran baƙi duk ya rataya a wuyan Galadima tun daga ranar da baƙi suka zo har su tafi.
  4. Ciroma: Ciroma shi ne mataimakin sarki na biyu, wanda idan babu sarki kuma babu waziri shi yake riƙe masarauta.
  5. Zanna: Shi ne yake kula da harkokin naɗe-naɗen sauran muƙamai da kuma ƙulla dangantaka tsakanin wannan masarauta da sauran jama’a kamar shirya ziyarce-ziyarce da gaishe-gaishen marasa lafiya da sauran dangogin su.
  6. Ciyaman: Shi ciyaman shi ne shugaban hakiman wannan masarauta. Ta hannunsa sarki yake saduwa da hakimansa. Idan sarki yana son isar da saƙo gare su domin su isar ga jama’a, to shi yake miƙawa. Haka nan suma hakiman ta hannunsa suke kai wa ga sarki.
  7. Turaki: Shi ne mashawarcin sarki na musamman. Shi ne mutum na ƙarshe da sarki yake tuntuɓa kafin ɗaukar mataki a koma wane irin hali ne.
  8. Sakatarori: Masarautar Shuwa Arab tana da sakatarori guda uku; babban sakatare guda ɗaya da kuma mataimakansa guda biyu. Dukkan alhakin rubuce-rubuce da kuma wallafe-wallafen wannan masarauta yana wuyansu.
  9. Kwamatin Mashawarta: Kwamati ne da ke tantance dukkan ayyukan masarauta tare da bai wa sarki shawara domin aiki ya tafi daidai.
  10.  Hakimai: Su ne wakilan sarki a sassan Lagos. Su ke gudanar da harkokin jama’a a ɗan ƙaramin mataki. Suna da dama ta gudanar da sasanto a tsakanin jama’a a kan rigimar da bata girmama ba.

Manazarta:


Tattaunawa da Sultan Jibril Yahya Ibrahim a Fadarsa da ke Lagos a Ranar Asabar 29/2/2020

Tattaunawa da Alhaji Ahmad Turakin Masarautar Shuwa Arab ta Lagos a Fadar Masarautar da ke Lagos a Ranar Lahdi 1/3/2020  




Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub